Yahuza Zaki Gwandu: Rashin Tsaro Laifin Shuwagabanni ne

Ra’ayoyinku - Yahuza Zaki Gwandu

Hakika VOA wannan matsala tana da matuqar ban mamaki.

Ni agaskiya babu wadanda na azama laifi da wuce gwamnoninmu, da sanatoci, da ‘yanmajalisu da ma sarakunanmu.

Domin bazai yiyu suce mana wai suna magana akan wannan matsala ba, shin shi shugaban kasa yafi karfin sune?

Sannan ina dukiyoyin talakawa dake hannunsu?

Don me baza suyi amfani da dukiyar talakawa ba domin nema mana tsaron dukiyarmu da rayukanmu?

Don me baza su je kasashen waje su sayo kayan aiki na zamani ba domin yin amfani dasu wajen leqen asiri akan harkokin tsaro?

Yakamata suyi amfani da wasu daga shawarwarinmu domin samun zaman lafiya ac ikin arewa da kasarmu baki daya.

---------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------


Sakonni da Masu Amfani da Shafi Suka Aiko

Muryar Amurka da Shafukan yanar Gizo masu dauke da bayanai, na iya barin masu anfani da kafar su rubuta ra’ayoyinsu su saka abubuwan da suka rubuta su yi sharhi, su aika da sakonni da hotuna da zane-zane da saka labarai da ma ire-irensu a matsayin bayanai da masu amfani suka aiko. To sai dai ka amince cewa duk abun da ka rubuta zai bi namu hanyar sadarwa ko wasu da muke muamala da su, su yi a madadinmu da yanar gizo. Ka amince cewa Muryar Amurka da kafar Sadarwa ta Yanar Gizo kafofi ne na anfanin jama’a ba hanyoyin sadarwar mallakar wasu ba ne.

Kana iya aiko da bayanai kamar wato abubuwan da ka rubuta wa Murya Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo wadanda mallakarka ne, wato kai ne ka rubuta, ko kuma kana da izinin marubucin ka yadasu ta yanar gizo. Ba zaka karya dokar da ta hana satar abun da wani ya rubuta ba ko ka hana wani hakkin gudunmawarsa game da rubutun wanda ya hada da ikon mallaka kamar sunan da wani ya yi rajista dashi domin aikin ko tambari da yake anfani da shi. Haka ma ba zaka saci asirin sana’arsa ba ko na kansa ko na talla. Ka yarda kuma ka tabbatar kai ne kake da iko da kuma izinin yin anfani ko yada ayyukan kuma ka baiwa Muryar Amurka izinin yada abun da ka rubuta.

Ka adana duk wata shaidar mallaka da kake da ita bisa ga duk ayyukan daka sa a Muryar Amurka da kafar Sadarwar Yanar Gizo. Amma domin ka baiwa Muryar Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo, to ka baiwa VOA ikon mallaka ita kadai na har abada ba tare da biyan wani haraji ba. Kuma zata yi anfani da shi duk fadin duniya, ta iya kofa, ko ta baiwa wani ko ta yi masa ‘yar kwaskwarima a yi anfani da shi a bainar jama’a da yin anfani da shi ta wasu hanyoyi daban daban.