Yadda Ziyarar Buratai Zuwa Sokoto Ta Kaya

Janar Tukur Buratai

Babban Hafsan Mayakan Sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya ziyarci jihar Sokoto wacce ke fama da dumbin matsalolin tsaro.

Ziyarar ta samu wakilcin kwamandan cibiyar horas da sojoji dake kontagora, Manjo Janar Muhammad Mahmood Mashellia.

Buratai ya ce duk da matsalar rashin tsaro da ake fuskanta, abin farin ciki ne ganin ba a manta da kulawa da jin dadin soji ba, kuma wannan zai iya kara musu kwarin gwiwa a aikin da suke yi na dakile ayyukan ta'addanci, satar mutane da kuma satar dabbobi.

Nuruddeen Bodinga, mai sharhi akan harkokin tsaro, yace wannan ziyarar ba shakka za ta kara kwazon sojoji suyi aiki yadda ya kamata.

"Soji kamar suna sayar da rayuwarsu ne, saboda haka dole ne a basu kulawar da ta dace."

Duk da kokarin da gwamnatoci ke yi na shawo kan matsalar rashin tsaro a yankunan gabashin Sokoto, mutane a wasu kauyuka na ci gaba da fuskantar barazana daga yan bindiga.

Ko a kwanakin nan mutanen kauyen Labau sun samu sako daga wasu 'yan bindiga na barazana a cewar shugaban kungiyar 'yan banga na kauyen Malam Sani.

Ga Mohammed Nasir da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Janar Buratai ya ziyarci Sakkwato