A jihar Katsina kayan aiki da ma’aikatan zabe tare da wakilan jam’iyyu wato “Agent” da kuma jami’an tsaro duk sun isa tashoshin zabe da misalin karfe bakwai, kuma an fara aikin zaben ne da misalin karfe takwas a akasarin tashoshin kada kuri’u dake fadin jihar.
A runfa mai lamba ta 003 inda shugaba Najeriya muhammadu Buhari yake kada kuri’arsa, ya iso wannan wuri da misalin karfe takwas da minti goma tare dashi Uwargidansa Hajiya Aishatu Buhari, sun isa wannan wuri kuma aka tantancewsu anan take, sannan aka basu kuri’un su sukaje ta fara kadawa bayannan shima shugaba Buhari ya kada nashi.
A lokacin zantawarsa da manema labarai shugaba Buhari ya godewa Allah, sannan ya godewa ga jama’an da suka fito sukayi dafifi a tsahar da yake jefa kuri’ar sa.
Kana kuma da manema labarai suka tambaye shi game da harkar tsaro yadda ya gudana a tashoshin zabe na Najeriya, shugaba Buhari yace ai wannan aiki ne na jami’an tsaro kuma yayi amannar cewa suna gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata.
Da misalin karfe goma sha daya da minti biyar ake tantance Gwamna jihar Aminu Bello Masari inda yake kada kuri’ar sa a garin Kafur dake kusa da gidanshi dake Masari, sannan yaje ya kada kuri’ar sa.
Lokacin da yake zantawa da manema labarai ya ce mutane sun fito gwargwadon hali kamar yadda ya gani a mazabarsa, a sauran mazabu ma hakan take. Kuma ana san ran za’ayi zabe lafiya a gama lafiya. Sannan yana kira ga jama’a da sukayi dafifi suka fito domin kada kuri’ar cewa zasu rubanya akan ayyukan da sukayi musu.
Ga dai Sani Malumfashi wakilin Muryar Amurka da cikakken Rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5