Hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka a Najeria ta NCDC, ta fitar da matakan da jama’ar kasar za su bi domin kare kansu daga kamuwa da sabuwar cutar “Coronavirus.”
Cutar Coronavirus, wacce ta bulla a kasar China a farkon watan nan, ta halaka mutum 17 kana wasu mutum sama da 400 na dauke da cutar.
Alamomin cutar sun hada da tari da matsalar yin numfashi.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Laraba, ta zayyana wadannan matakan dakile yadawa da kamuwa da cutar a tsakanin al’uma:
- Wanke hannaye akai-akai da sabulu da kuma ruwa mai gudana
- Rufe baki da hanci (da hankici) a duk lokacin da mutum zai yi tari ko atishawa.
- Mutum zai iya amfani da jikin hannunsa ya kare bakinsa idan zai yi atishawa – ko da babu hankici.
- Ku guji yi wa kanku magani, ku garzaya asibiti mafi kusa idan kun ji alamar cutar, kamar tari ko matsalar yin numfashi.
- Jami’an kiwon lafiya su bi ka’idojin da aka shimfida wajen gujewa kamuwa da cuta idan suna kulawa da marasa lafiya, sannan su bibiyi wuraren da mara lafiyan ya je a baya.
Sannan sanarwar ta NCDC, ta kara da cewa tana kan samar da wata tawagar kwararru wacce za ta sa ido kan yiwuwar bullar cutar a Najeriya tare da dakile hanyoyin da za a iya shiga da ita cikin kasar.