Wasu ‘’yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu dalibai yara ‘yan makaranta akalla su biyar a karamar hukumar Obio Akpor dake Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya.
‘Yan bindigan dai kawo yanzu ba’a kai ga gane su ba, kuma suna ci gaba da garkuwa da yaran a cikin surkukin dajin yankin na Naija Dalta.
“Muna cikin kaduwa sosai kan wannan al’amari da ya auku kuma yarona yana cikin mutane biyar da aka yi garkuwa da su. Kuma wani abun mamaki shi ne ba’a makaranta aka dauke su ba an dauke su ne mafi yawanci a gidanjensu, a kuma lokuta daban daban. Mu iyaye muna ciki halin kaka ni kayi, Muna kira ga hukumomi da su tashi tsaye dan ganin an ceto yaranmu.” In ji Mister Tony Benson, daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da ‘ya’yansu.
Rundunan ‘Yan sandan Jihar Rivers ta Tabbatar da lamarin. DSP Grace koko ita ce mai Magana da yawon rundunan ‘Yan sandan. Ta ce
“Bisa ga yara da aka yi garukuwa da su ‘Yan makaranta, wannan lamarin ya faru sannan kuma ina so in tabbatar maka da cewa a tsaye muke dan ganin an ceto su, kawo yanzu bamu kai ga kama kowa ba.”
Farfesa Bello Bada, malami ne a Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo dake Sokoto kuma mai sharhi a al’amuran yau da kullum, ya ce “ba karfin hukumomin Najeriya aka fi ba, ko oho hukumomin Najeriya su ke yi. Duk wani wanda aka ba’a amana to kokari yake ya ga ya tara kazamin dukiya.”
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar Sokoto:
Your browser doesn’t support HTML5