Yadda Wata Gobara Ta Lakume Shaguna 30 a Nijar

Wata gobara ta lakume sama da shaguna 30 a birnin Maradi da ke Jamhuriyar Nijar.

Gobarar ta tashi ne a wata tashar motoci, wacce ta kasance cibiyar kasuwanci a kasar.

Bayanai sun yi nuni da cewa, wannan lamari ya jefa al’umar garin cikin yanayi na alhini.

“Muna zaune kawai wutar ta tashi, kuma duk shagon da ya kone yana cike da kaya. Wasu sun fidda wasu kaya wasu kuma ba su fitar da komai ba.” In ji Alhadji Dan Ada, wanda ya shaida lamarin.

Shi kuwa shugaban kungiyar adalci masu zirga-zirga Alhadji Sa'idu ya ce, duk da cewar an yi asarar dukiya, ya ji dadin yadda babu wanda ya rasa ransa.

“Babu wanda zai ce maka ga abin da ya haddasa wannan lamarin, ni kai na, sai dai kawai na ga wuta na ci, sai na ruga na fitar da mota ta daga cikin tasha kuma na bude kofar tashar domin ‘yan kwana - kwana su samu shigowa,” a cewar Alhadji Sa’idu.

Wannan shi ne karo na biyu a kasa da wata guda da wannan tashar ta garin Maradi ke fuskantar irin wannan ibtila’i.