A kasar Kamaru, wasu mata kan dogara ne da ayyuka masu matukar wuya wajen neman kudaden da za su biya bukantunsu na yau da kullum.
A yankin Arewa mai Nisa, wasu mata magidanta kan kwashe yini suna aikin fasa duwatsu don su sayar su samu na biyawa iyalansu bukata.
Hakan ya sa a wannan yanki, aka yi kiyasin mata na daga cikin rukunin masu tallafawa tattalin arziki a yankin Arewa mai nisa.
Mafi akasarin matan da ke wannan sana’a sun shige ta ne a dalilin matsanancin halin rayuwa kamar na talauci.
Dutsen Misengelo da ke Arewa mai Nisan, shi ne shararraen wuri da akan tarar da ire-iren wadannan mata wadanda kan kwashe yini suna aikin fasa duwatsu.
“Sai mun fasa dutse kafin mu samu abin kashewa” In ji wata daga cikin matan da ba ta bayyana sunanta ba.
Matan kan gudanar da wannan aiki ne ko a wane irin hali na yanayi da ake ciki, kamar na rana ko ruwa ko sanyi.
“Yara takwas ne a karkashina, akwai yaran wasu matan da suka yi gudun hijira, saboda haka, ya zama dole na fito na yi wannan aiki don na kula da su.” In ji Anita wacce ta kwashe sama da shekaru 20 tana wannan sana’a.
A cewar Anita, ba a samun kudi mai yawa a wannan sana’a, amma kuma ana samun rufin asiri.
Saurari cikakken rahoton Mohamadou Rabiou:
Your browser doesn’t support HTML5