Yadda Tsohon Sarkin Kano Ya Isa Legas

Maimartaba Muhammadu Sanusi II, sarki na 14

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, sarki na 14 ya isa birnin Legas da ke kudancin Najeria, bayan da ya baro filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, babban birnin kasar.

Wata kotu a Abujan ce ta ba da umurnin a saki Malam Sanusi bayan da gwamnatin Kano ta sa shi karkashin daurin talala, jim kadan bayan da ta sauke shi daga mukaminsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, sarki Sanusi ya baro birnin Abuja ne da misalin karfe 10:15 na dare a wani jirgin shata ya kuma isa Legas ne da misalin karfe 11:35 na dare.

Sanusi ya samu rakiyar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i wanda ya raka shi har kofar jirginsa a Abuja.

Bayan da ta tsige shi, gwamnatin jihar Kano ta ba da umurnin a kai sarkin garin Loko da ke jihar Nasararwa, inda daga baya aka sauya mai gari aka mayar da shi Awe.

Shafin yanar gizo na gidan talbijin din Channels, ya ruwaito cewa Alkali Anwuli Chikere ya ba da umurnin sakin sarkin, bayan da lauyoyinsa suka shigar da kara kan abin da suka kira take mai hakkinsa na walwala.

A ranar Litinin din da ta gabata, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano, ya ba da umurnin tsige Sanusi a matsayin sarkin Kano, bisa dalilai da ya ayyana a matsayin na rashin mutunta gwamnatinsa, tare da kin yi mata biyayya da sarkin ya yi.

An dai jima ana ta kai ruwa rana tsakanin masarautar Kanon karkashin Sanusi da gwamnatin Ganduje.

An nada Muhammadu Sanusi II ne a matsayin sarkin Kano a shekarar 2014.