Yadda Ta Kaya A Fafatawar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai

A ci gaba da fafatawa da ake yi a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai na shekara 2018 zuwa 2019 a matakin wasan rukuni zagaye na uku a ranar Talata Manchester United ta kasar Ingila ta sha kashi a hannun Juventus, ta kasar Italiya da kwallo daya mai ban haushi.

Dan wasan Juventus Poulo Dybala shi ya jefa kwallon a cikin minti na 17 da fara wasan kafin tafiya hutun rabin lokaci a ragar United.

Roma ta lallasa CSKA Moscow da ci 3-0, Shakhtar Donetsk, Manchester City ta lallasa ta da kwallaye 3-0 sai Ajax ta doke Benfica da ci 1-0

A sauran wasanni kuwa kungiyar kwallon kafa ta Hoffenhiem sun yi canjaras 3-3 da Lyon, Young Boy 1-1 Valencia, AEK Ethens 0-2 Bayern Munich, Real Madrid ta samu nasara akan Viktoria Plzen da ci 2-1.

Ku Duba Wannan Ma Mesut Ozil Ya Kafa Tarihi a Duniyar Tamaula

Dan wasan gaba na Real Kareem Benzema ne ya fara jefa kwallo a minti na 11 da fara wasan sai kuma Marcelor ya jefa ta biyu a minti na 55 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Daga bisani, Viktoria ta farke kwallo guda ta kafar dan wasanta Hrosovsky a minti na 79.

A yau za'a ci gaba da fafatawa a sauran wasannin inda da misalin karfe 5:55 na yammaci agogon Najeriya da Nijar.

PSV za ta karbi bakuncin Tottenham, sai kuma Club Brugge da Monaco,

Da misalin karfe takwas na yammaci kuwa Barcelona zata kece raini da Inter Milan, sai kuma Borusia Dortmund da Athletico Madrid , PSG da Napoli,

A can kasar Ingila kuwa Liverpool zata karbi bakunincin Crvena Zvezda, sai kuma Lokomotiv Moscow, zata kara da Fc Porto a kasar Rasha, sai Galatasaray da Shalke 04.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Zata Kaya A Cigaba Da Fafatawar Cin Kofin Zakarun Turai 2'30"