Dan wasan baya na Arsenal Laurent Koscielny da yuwuwar ba zai samu damar fafata wa a kasar Faransa ba, a wasan cin kofin duniya da za a yi na 2018, a can kasar Rasha Sakamakon raunin da dan wasan ya samu a wasan da suka yi da Atletico Madrid na dab da na karshe a kofin Europe, karawa ta biyu ranar Alhamis inda aka doke Arsenal daci 1-0.
Laurent Koscielny, ya fice daga wasan a minti na 12 da farawa saboda ciwon da ya ji a tafin sawun sa, wanda ake ganin mafi yawancin wannan jinya kan dauki wata shida ne kafin dawowa wasa a fili.
Arsenal, dai ta fice daga gasar ta Europe bisa jimillar kwallaye 2-1 inda a karawar su ta farko aka yi 1-1 a Ingila. Sai dai tana da sauran wasanni uku ta kammala wasaninta na Firimiya lig na kasar Ingila a bana.
Arsenal dai tana mataki na 6 a teburin da maki 57 a kasan Chelsea, wace ta ke da maki 66 sai Burnley ta ke biye da ita da maki 54.
Bayern Munich, ta ce tana bukatar dauko dan wasan gaba na Juventus, Paulo Dybala, mai shekaru 24, in har dan wasanta Robert Lewandowski, dan shekara 29, ya bar kungiyar a karshen kakar wasan bana.
Kocin Manchester United, José Mourinho ya sake bayyana ra'ayin sa na dauko matashin dan wasan gaba daga kungiyar Ajax mai suna Justin Kluivert, mai shekaru 18 ga haihuwa da ga Patrick Kluivert.
Arsenal ta shiga gaban Bayern Munich, wajan sayen dan wasan baya, dan kasar turkiya mai suna Caglar Soyuncu, wanda yanzu yake buga wasansa a kungiyar Freiburg ta kasar Jamus.
Your browser doesn’t support HTML5