Kocin kwallon Najeriya Gernot Rohr, ya ce Super Eagles na da kyakkyawar makoma bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Brazil a wasan sada zumunta na kasa da kasa a jiya Lahadi a kasar Singapore.
'Yan wasan sun nuna kokarinsu da kansu tare da Joe Aribo – wanda wannan ita ce fitowarsa a karo na biyu ga kungiyar ta Super Eagles – yayin da ya jefa kwallon farko a cikin minti 35 kafin Casemiro ya mayarwa da ƙungiyar kwallon ta Kudancin Amurka martani.
Kunnen doki dai ita ce ta biyu a jere ga kungiyar ta Brazil ta yi, bayan da Senegal ta rike su a wasan sada zumunta a ranar Alhamis.
Rohr ya yi matukar farin ciki da yadda kungiyar tasa ta taka leda, amma ya ce yakamata kungiyar wadda ta zama zakara har sau uku, na kwallon zakaru na Afirka, ta ci gaba da ingantawa.
Rohr ya ce "Abu ne mai wahala a garemu a matsayin wasa na biyu saboda Brazil ba za ta so ta bar Singapore ba tare da cin nasara ba, kuma na yi matukar farin cikin sanin cewa za mu iya taka leda sosai da manyan masu suna a kwallon kafa," in ji Rohr a wani taron manema labarai.
"Kwararrun 'yan wasan kungiyar ma basa nan, amma duk da haka, mun ba wa Brazil wahala sosai da kariya, kuma 'yan wasanmu sun faranta mun rai matuka. Za su iya samun makoma mai kyau."
Rohr ya yi imanin cewa kwallon kafa ta Afirka na inganta bayan Najeriya da Senegal suka kaurace wa ci a hannun zakaru na uku na duniya.
Ya kara da cewa "Wadannan sakamakon suna da kyau ga kwallon kafa ta Afirka idan har Senegal da Najeriya ba su sha dokewa ba daga hannun Brazil, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallo a duniya."
Najeriya za ta yi fatan samun kyakkyawan sakamako idan har suka gana da Jamhuriyar Benin da kuma Lesotho a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afirka a watan Nuwamba.