Wasu kusoshin jam'iyyar a jihar Taraba sun kira wani taron manema labarai domin maida martani ga shugabannin jam'iyyar na jihar.
Alhaji Yau Sama'ila Mayus wani kusa a jam'iyyar yace su suna tare da zabin da shugaba Buhari yayi. Yace kushewa zabin da shugaba Buhari yayi ra'ayin shugabannin jam'iyyar APC ne amma ba ra'ayin jam'iyyar ba ne, ba kuma ra'ayin 'yan jam'iyyar ba ne a duk fadin jihar gaba daya.
A cewar Alhaji Mayus shugaba Buhari yana zakulo wadanda suka san abun da su keyi ne ba wadanda suke son kansu ba, wadanda basa kula da jama'a. Ya kara da cewa ita jam'iyyar ma a jihar Taraba ta wargaje.
Shi ma wani jigon jam'iyyar Umar A Umar ya kara haske game da wannan takunsakar. Yace "cewar jam'iyyar APC gaba daya bata yadda da zabin ba ba haka ba ne". Yace da maganar ta taso sun zauna da shugaban jam'iyyar na jiha Alhaji Ardo. Yace su suna yiwa Buhari biyayya domin "biyayya gareshi biyayya ga Allah ne", inji Umar.
To saidai shugabannin hadin kan jam'iyyun da suka zama APC sun mayar da martani akan kalaman. Alhaji Abdullahi Adi shugaban matasa na jam'iyyar ya bayyana matsayinsu tare da cewa wadanda suka yi magana 'yan neman tuwo ne. Basa cikin APC. Amma har yanzu suna kan bakarsu. Basu yadda da wanda Buhari ya nada ba domin basu sanshi ba. Mutumin, injisu har yanzu yana cikin jam'iyyar PDP.
'Dan majalisar dattawa daga jihar kuma dan APC Yusuf A Yusif yace shugaban kasa dana dama ya ba duk wanda ya ga dama ya kuma cancanta mukamin siyasa amma dole a bi ka'ida. Yace a yiwa mutane adalci ta zama dasu a san wandanda suka yiwa jam'iyya da mutane aiki a kuma duba cancantarsu. Idan ba'a yi haka ba, to ba'a yiwa mutane adalci ba.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5