Yadda Rikici Ya Janyo Aka Kafa Dokar Hana Fita a Garuruwa 11 a Adamawa

Wani mai zanga-zanga a kasar Falasdinu

Gwamnatin jihar Adamawa ta kafa dokar hana fita na ba dare ba rana a garuruwa 11 na yankin karamar hukumar Guyuk da kuma wani gefe na Lafiya Lamurde sakamakon wanni tashin hankali da ya auku a tsakanin kabilu na Lunguy da Waja.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar rikicin ya taso ne kan takaddamar filayen noma, wanda kuma ya jawo asarar rayuka da kuma dukiya.

Mr Solomon Kumangar daraktan yada labaran gwamnan jihar ya bayyana manufar wannan dokar hana fitan.

"An dauki wannan matakin saboda tarzomar da ta barke domin a kwantar da ita, kwannakin baya ma an samu irin wannan lamarin amma dokar hana fitan da aka kafa ce ta kawo sauki ko a lokacin."

Ya kara da bayana yadda mataimakin gwamnan jihar ya ziyarci wuraren da lamarin ya faru domin kai musu tallafi.

Wani wanda a yanzu yake gudun hijira sanadiyar wannan rikici ya shaida mana cewa da shi da mutane da yawa sun gudu sun nemi mafaka a kauyukan da ke makwabtaka da garuruwansu.

Ya zuwa yanzu rundunar Yan sandan jihar Adamawa tace ta kama sama da mutum talatin da ake zargin suna da hannu a wannan lamarin.