Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi Jihar Katsina

Mazauna yankunan jihar Katsina na ci gaba da zama cikin yanayi na zullumi da fargaba sanadiyyar harin ‘yan bindiga da ke satar jama’a don karbar kudin fansa da ake yi.

Khalid Adamu, mazaunin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa masu garkuwa da ne suka fi addabar yankinsu.

“Wasu ‘yan bindiga sun sace kannenmu guda biyu ana jibi aurensu a garin Yankara bayan kwana biyu kuma suka sake dawowa suka sace wasu mutum uku" a cewar Khalid.

Wani da ya so a sakaya sunansa, shi kuma cewa ya yi akwai garin da ‘yan bindigar suke zama a karamar hukumar Batsari, suna sanya kayan sojoji dauke kuma da bindigogi.

A wata hira da Muryar Amurka, shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Rimi, Honarable Abubakar Suleiman Abukur, ya ce sun yi shawara sun kuma bukaci gwamnan jihar ya ba da dama jama’a su kare kansu, saboda a cewarsa kamar an sami tsaiko daga gwamnatin tarayya wajen daukar matakan.

Ya kuma ce ya kamata Babban Hafsan sojojin Najeriya ya tare a jihar Katsina don yaki da maharan kamar yadda aka yi a jihar Borno don yaki da 'yan Boko Haram.

Ya kara da cewa, da suna da iko a matsayinsu na ‘yan majalisar jiha da za su yi dokar da za ta ba da dama a yi ‘yan sandan jiha amma hakan zai yi karo da kundin tsarin mulkin kasa.

Game da batun samar da jami’an tsaron yanki da gwamnoni suka tattauna a kai a baya, Honarable ya ce ta yi wu wannan matakin ya dauki lokaci mai tsawo, don haka ya kamata a dauki matakin gaggawa akan jihar Katsina saboda yanayin da jama’a ke ciki.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Sani Shu’aibu Malumfashi.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi Jihar Katsina