Yadda Matsalar Fyade Ke Kara Ta'azzara a Najeriya

Cin zarafin mata ta hanyar fade, batu ne da ke ci gaba zama ruwan dare a Najeriya inda a 'yan kwanakin nan matsalar take kara bulla a wasu jihohin kasar.

A jihar Kaduna da ke arewacin kasar an samu rahoton wasu gungun maza su hudu da suka aikata fyade akan wata yarinya 'yar kimanin shekara 13 da haihuwa bayan sun dirka mata kayan maye, suka kuma jefar da ita a karkashin wata mota a kusa da gidan iyayenta.

A birnin Ibadan na jihar Oyo an bugawa wata matashiya dutse a kai bayan an mata fyade lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.

Tuni dai masu rajin kare hakkin bil adama da dama irinsu Bushira Balonun suka fito suna kira ga gwamnatoci da su tashi tsaye kajen yaki da wannnan mummunar dabi'a.

Amina yahaya wacce aka fi sani da sarauniyar Arewa da ke fafutukar kare hakkin mata a Najeriya ita ma ta ce wannan matsalar ta fyade na da ban tsoro, inda ta kara da cewa rashin hukunta wadanda ke aikata wannan mummunan aika-aika ne ya sa matsalar ke ci gaba da kazancewa.

Cikin wani binciken cin zarafin yara a Najeriya an bayyana cewa 1 cikin yara mata 4 da kuma 1 cikin yara maza 10 suna fuskantar cin zarafi kafin su kai shekaru 18 ta ko wacce irin hanya.

Sannan fiye da kashi 95 cikin 100 na yara da ake cin zarafin su, wandanda suke makusantansu ne ko 'yan uwa na jini ko cikin dangi suke aikata wannan mumumnan aiki.

Tsare-tsare na dokikin Majalisar Dinkin Duniya da kuma na kasashen Afirka sun yi hani akan aikata fyade, inda aka tsananta mutunta hakkin bil adama a duk inda yake.

hakan ya sa masana shari'a irinsu Barrister Umar Mai Nasara Faskari suka yi kira da a yi wa dokokin hunkunta laifin fyade garambawul.

Daga karshe kungiyoyi da dama na mata sun yi kira ga iyaye mata da ake cin zarafin 'ya'yansu ta hanyar fyade da su ringa kai rahoto ga hukumomin tsaro domin yin rufa-rufa ka iya ta’azzara matsalar ta fyade a cikin al’umma.

Saurara karin bayani daga Shamsiyya Hamza Ibrahim a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Matsalar Fyade Ke Kara Ta'azzara a Najeriya