Yadda Mata Masu Matsalar Yoyon Fitsari Ke Fuskantar Tsangwama

Tsangwama da ake nunawa mata masu cutar yoyon fitsari na haifar da koma baya ga zamantakewar iyalai.

Masu matsalar cutar yoyon fitsari na fuskantar matsananciyar tsangwama daga makusantansu, lamarin da ke kara janyo nakasu ga zamantakewar iyalai.

Alkaluman da hukumar lafiya ta Global Health ta wallafa na nuni da cewar, Najeriya ce ke kan gaba cikin kasashen duniya da ke da masu dauke da cutar, tsakanin mata 800,000, zuwa miliyan daya, ana kuma samun mata 20,000 da ke samun cutar yoyon fitsari a kowace shekara.

Cibiyar tallafawa masu dauke da cutar yoyon fitsari da ke asibitin kwararru ta Jami’ar Bingham, wanda aka fi sani da asibitin Jan kwano a birnin Jos ta gudanar da aikin tiyata ga mata da dama da ke dauke da cutar, wanda kuma suka samu waraka daga cutar.

Wasu daga cikin masu dauke da wannan cutar, da aka yi wa aiki, sun bayyana irin halin da suke ciki.

Esta Monday, ta ce tun bayan da aka yi mata aiki ta kamu da wannan cutar, wanda har sai da ta kai mijinta ya gujeta haka ma iyayen ta ma suka ce mata tana warin fitsari.

Hakan ya saka rayuwarta cikin kunci, amma yanzu an yi mata aiki kyauta a wannan asibitin.

Haka ita ma Beauty Bakuwa, ta samu matsalar hatsari, wanda daga nan ta kamu da wannan cutar, amma yanzu haka an yi mata aiki, ita ma mijinta ya kaurace mata. Yanzu haka ma ta samu labarin cewar zai yi aure, don irin halin da take ciki.

Ita ma Susana Kepas, wadda ta ce sanadiyyar kamuwar ta da wannan cutar shi ne, a lokacin da ta zo haihuwa ta yi nakuda mai tsawo, na tsawon kwanaki, wanda hakan ya haifar mata da wannan matsalar. Ba ta kuma samun gudunmowa daga wajen kowa.

A ta bakin daraktar cibiyar Madam Angelina Ozim, suna samun mutane daga kasashen waje, da kan zo don samun taimako.

Mafi akasarin wadannan matan suna fuskantar tsangwama daga wajen 'yan uwansu. Don haka suna kira da mahukunta su taimaka wajen ganin an baiwa mata masu dauke da irin wannan matsalolin kulawa da suke bukata.

Ga rahoton Zainab babaji a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Mata Masu Matsalar Yoyon Fitsari Ke Fuskantar Tsangwama