Yadda Masu Zabe A Karon Farko Suke Ji

Wata 'yar takara neman kujerar majalisar jihar a Kano Zainab Sulaiman Umar, mai shekaru 26.

Daga cikin 'Yan Najeriya sama da mutum miliyan 80 da ake sa ran za su zabe a yau, akwai miliyoyi daga cikinsu da wannan zabe zai zamanto na farko a rayuwarsu musamman ma matasa.

Da yawa daga cikin ire-iren wadannan mutane, wadanda galibinsu matasa ne, sun nuna matukar jin dadi kan yadda a karon farko a rayuwarsu, sun samu damar kada kuri’a.

“Gaskiya ina jin dadi, ina farin ciki, a matsayi na wacce za ta fara yin zabe a karon farko, zan zabi ra’ayi na zan zabi wanda na ke so a matsayin shugaban kasa.” Inji Asiya Adamu.

Mafi aksarin wadannan matasa, ba su kai shekarun da za su kada kuri’a ba a zabukan da suka gabata.

“Wannan ne karon na farko da na mallaki katin zabena, kuma na yi shiri zan kada kuri’ata. Ina matukar farin ciki saboda wannan ne karo na farko da zan kada kuri’a” Inji Abdulbasit Umar mai shekaru 22.

Ita kuwa Maryam Sa’id Umar wacce ta yi magana da VOA cikin yanayi na annashuwa, cewa ta yi “wannan wata babbar dama ce, a ce ka zabi mutum, kuma a ce mutumin kirki, ka ga ai wannan babbar dama ce.”

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Masu Zabe A Karon Farko Suke Ji - 2'42"