Yadda Jam’iyyu Ke Fadi-tashin Ganin Sun Lashe Zabe A Jihohi Biyar

Wani gangamin siyasa a zaben 2019

Yanzu a jihohi 5 cikin 6 za a kammala zaben gwamnoni bayan matakin ci gaba da kidayar kuri’u a jihar Bauchi da yiwuwar samun sakamako a Talatar nan

Bayan matakin hukumar zaben Najeriya INEC na ci gaba da kidayar kuri’u a karamar hukumar Tafawa Balewa a Bauchi da yiwuwar samun sakamakon a Talatar nan, hankali ya koma kan jihohi 5 da za a kammala zaben gwamnoninsu ranar Asabar da su ka hada da Adamawa, Binuwai, Filato, Kano da Sokoto.

APC ta ki amincewa da matakin hukumar zaben a Bauchi da ta ke fargabar ya bai wa PDP damar nasara ta hanyar da sai kotu ce za ta yanke hukunci.

A jihar Kano madugun PDP Rabiu Musa Kwankwaso ya ce tazarar da su ka ba wa APC ta fi yawan kuri’u da a ka soke da hakan ke nuna da PDP za ta so a dau mataki irin na Bauchi.

Da ya ke maida martani kan rade-radin samun sabani da APC, tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya ce kage aka yi ma sa kuma ya na bukatar a fito don zabar APC ranar asabar.

Wani abu kuma da ke alaka da dambarwar sakamakon zaben shi ne shirin tafiya kotu da wadanda ba su gamsu ba ke shirin yi.

Sanata Sani Danladi da ya yi wa APC takarar gwamna a Taraba ya ce in da an yi adalci da zai iya rungumar kaddara.

Yanzu dai za a jira matakin hukumar zaben kan jihar Ribas a ranar Laraba bayan samun rahoton kwamitin da ya bincika birkita zaben jihar.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Jam’iyyu Ke Fadi-tashin Ganin Sun Lashe Zabe A JIhohi Biyar - 2'58"