Gobara ta yi barna mai matukar yawa ga sananniyar majami’ar nan ta Notre Dame Chathedral da ke birnin Paris.
Amma ‘yan kwana-kwana sun ce sun kare hasumiyoyi biyu na ginin, da kuma wani ginin dutse.
Shugaban hukumar kashe gobara ta birnin Paris Jean-Claude Gallet, ya fadawa manema labarai a gaban ginin a jiya Litini cewa, an kare muhimman ginshikan da ke rike da ginin.
Ya ce daya daga cikin ‘yan kwana-kwanan ya ji mummunan rauni yayin da ake kokarin kashe wannan babbar gobara a babban birnin na kasar Faransa.
Wutar, wadda a wani lokaci sai da ta yi sama da tsawon mita 10, ta lalata akasarin rufin majami’ar inda har hasumiyar rufin ta fadi.
Mai magana da yawun hukumar majami’ar, Andre Finot, ya gaya ma kafafen labaran Faransa jiya Litini cewa, ga dukkan alamu sai an karasa rusa duk wani abu dangin katako na cikin ginin majami’ar.