Yadda Fashewar Tukwanen Iskar Gas Ta Lalata Gidaje 50 a Legas

Mutane kenan yayin da suke wuce wurin da lamarin ya faru.

Mutane da dama ne ake kyautata zaton sun rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta auku bayan da wasu tukwanen iskar gas suka fashe a Abule Ado da ke jihar Legas a jiya. 

A kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu, yayin da gidaje 50 suka kone kurmus.

Haka kuma ababen hawa da ke yankin suma sun wargaje sakamakon karfin fashewar.


Mr tunji Disu, babban jami’in ‘yan sanda da ke saka ido a yankin da lamarin ya auku, ya shaida wa manema labarai cewar ana ci gaba da kokarin kashe wutar da ta tashi a yankin.


Shi kuwa, kwamishinan yan sanda a yankin ya umarci ‘yan sanda a kalla 500 da su saka ido wurin da lamarin ya faru.

Mutanen da suka samu raunuka dai na can asibiti suna jinya.

Babban kamfanin man fetur na Najeriya ya fitar da sanarwa inda ya ce fashewar bata da alaka da fashewar bututun man kamfanin, kamar yadda tun farko wasu al’umma ke fadi.

Kamfanin na NNPC ya kuma kara da cewa hatsarin ya auku ne sakamakon fashewar tukwanen gas a wata tashar sayar da iskar gas, da ke kusa da inda bututun man kamfanin ya ke.


Wannan dai ba shine karon farko da ake samun fashewar bututun mai ko na tukwanen iskar gas ba a jihar ta Legas.

Ko a farkon shekarar nan sai da fashewar bututun mai ta yi sanadin mutuwar mutum 3 da kona dukiyoyi na miliyoyin naira.

Bayan wannan lamarin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika da sakon jajantawa ga iyalan wadanda wannan hatsarin ya shafa.

Ya kuma ce kamfanin NNPC zai yi iya kokarinsa ya gano musabbabin wannan hatsari.

Ga cikakken rahoton a sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Fashewar Tukwanen Iskar Gas Ta Lalata Gidaje 50 a Legas