Facebook Ya Cire Bidiyon Wata Likitar Da Ta Yi Makaranta a Najeriya

Tambarin Facebook

Kamfanonin Facebook da Twitter da Youtube sun cire wani bidiyon wasu likitoci a Amurka bayan da ya karade shafukan sada zumunta.

Bidiyon ya nuna likitocin suna cewa maganin hydroxychloroquine yana warkar da mutane daga Cutar COVID-19.

Wani shafin intanet mai suna Breitbard News ne ya wallafa bidiyon wanda shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa mai mabiya miliyan 84.

A cikin bidiyon an ga yadda likitocin wadanda su ka kira kansu "American Frontline Doctors", suka tsaya a gaban ginin kotun kolin Amurka a birnin Washington DC suna magana.

Wata mai suna Stella Immanuel wacce ta ce ta yi karatun aikin likitanci a Najeriya na daya daga cikin likitocin.

A cewarta amfani da takunkumi baya hana yaduwar coronavirus, ta kuma kara da karyata duk wani binciken da ya nuna cewa maganin hydroxychloroquine ba ya magańce cutar.

"Cutar nan na da magani, ana kiransa hydroxychloroquine da Zinc da Zithromax," a cewarta.

Hakan na zuwa lokacin da masana kiwon lafiyan suke gargadin mutane kan amfani da hydroxychloroquine wajen kariya saboda rashin ingantaccen binciken da ya tabbatar da cewa maganin zai Iya warkar da masu Covid-19.