Yadda Canza Sheka Ke Shafar Tsarin Damokaradiyar Najeriya

hotunan yan siyasa

Batun sauya sheka al’amari ne daya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasa Najeriya tun gabanin jam’iyyun siyasar kasar su fara gudanar da zaben fitar da gwani domin tunkarar zaben shekara ta 2019. Sai dai masana kimiyyar siyasa na ganin hakan koma baya ne ga ci gaban demokaradiyyar kasar.

Tun bayan da Najeriya to koma tafarkin demokaradiyya kusan shekaru 20, manya, matsakaita da kananan ‘yan siyasa ke sauya sheka daga wannan Jam’iyya zuwa waccan.

Na baya bayan nan sun hada da gwamnan Sokoto Aminu Tambuwa da sanata Sulaiman Hunkuyi da Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara da Alhaji Ahmed Musa Ibeto tsohon jakadan Najeriya a Afrika ta kudu kana da sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dukkanin su daga Jam’iyyar APC zuwa PDP, yayin da Sanata Godswill Akpabio ya kaura daga PDP zuwa APC.

Bayan sauya sheka wasu ‘yan siyasar kanyi katari su dace bukata ta biya, wasu kuwa su gamu da akasin haka.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Canza sheka a Najeriya-4:00"