Yadda Aka Yi Wa Gwaggon Biri Tiyata A Ido

Gwaggon Biri

Tawagar shahararrun likitocin ido sun gudanar da tiyata ga wani mara lafiya da ba’a saba gani ba – gwaggon biri, wato 'Gorilla' a turance.

An gudanar da aikin ne a idon hagu na gwaggon birin, inda suka cire mata ‘yanar ido a cewar jami'ai.

Gwaggon birin wacce ke da shekaru 3 da haihuwa, na zaune ne a gidan ajiyar namun dawa ‘Zoo Safari’ da ke birnin San Diego a jihar California a Amurka.

Bayan aikin idon an rataya, gwaggon birin wacce aka yi wa inkiya da Leslie, wani abu da ke rufe idon, an kuma sauya mata wani bangaren idon ta da ke taimaka mata wajen gani, aka kuma saka mata wani na roba kana na din-din-din, don karawa idon karfin gani.

Daya daga cikin likitocin da suka gudanar da aiki, kuma wanda ya jagoranci tiyatar Dr. Chris Heichel, ya ce yayi tiyatar ido fiye da dubu, amma wannan shine karon farko da yayi tiyata ga dabba, kuma gwaggon biri.

Ya kara da cewar “Akwai kamannin matuka tsakanin idon mutum da na gwaggon biri, wanda hakan yasa bamu sha wahala ba wajen aikin.” Dayan idon nata bashi da matsala don kuwa tana gani da shi sosai.

Mafi yawanci yanar ido kan samu idan shekaru sun ja.

Amma ba mamaki gwaggon biri Leslie ta samu matsala a idon nata ne, lokacin da take koyon tsalle-tsalle, a cewar mahukunta gidan zoo din.

Likitoci sun rubuta mata magunguna da za ta sha da ke kashe kwayoyin cutar antibayotik don gujema kamuwa da wasu kananan cututtuka.