An yi jana’izar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe a kauyensu na Kutama, jana'izar da mutane kalilan ne suka halarta.
Marigayi Mugabe, wanda ya rasu yana da shekaru 95, shi ya zabi da a binne shi a kauyen na su, bayan da ya bar wasiyyar cewa kada a binne shi a wurin da aka saba binne gwarazan kasar a Harare babban birnin kasar.
Mugabe ya bar wasiyar ne saboda a cewar shi an “wulakanta shi” a lokacin kawar da gwamnatinsa.
Iyalan marigayi Mugabe ne kadai aka bari suka halarci wajen jana’izar.
Junior Shuvai Gumbochuma, kanwa ga Mugabe, ta ce burinsu ya cika domin sun bi wasiyyar dan uwansu.
Mugabe dai ya riga mu gidan gaskiya ne a wani asibiti da ke kasar Singapore a farkon watan nan, bayan kusan shekaru biyu da hambarar da gwamnatinsa wacce ta kwashe kusan shekaru 40 tana mulkar kasar.