Yadda Aka Samu Sarakuna Biyu A Karon Farko A Tarihin Masarautar Kano

Your browser doesn’t support HTML5

An samu sarakuna biyu da kowannensu ke zaman fada a matsayin sarkin Kano a lokaci guda. Yayin da Muhammadu Sanusi da gwamnatin jihar ta mayar da ya rika karbar gaisuwa da mubaya’a a babban gidan sarautar, shi kuwa Aminu Ado Bayero, ya rika yin na shi zaman fada ne a gidan sarki dake Nasarawa GRA.