‘Yan sanda a jihar Rivers da ke yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya, sun tabbatar da sace wasu ma’aikatan kamfanin mai na Shell.
Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ma’aikatan na Shell kwantan bauna, suka kashe ‘yan sandan da ke kare lafiyar ma’aikatan da direban motarsu suka yi awon gaba da su.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar Rumuji da ke karamar hukumar Aboa a yankin Ahoda ta Yamma.
“Lallai mun tabbatar da sace manyan ma’aikatan kamfanin man Shell…. Kuma a tsaye muke, mu tabbatar da cewa mun ceto su.” Inji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta rivers, Emoni Nnamdi.
Wani kakakin kamfanin man na Shell, shi ma ya tabbatar da aukuwar lamarin.
"Kamfanin man fetur na Shell da ke Najeriya, na cike da alhini yayin da yake tabbatar da harin da aka kai kan ma'aikatansa da jami'an tsaron na gwamnati a yankin Rumuji da ke jihar Rivers a kan hanyar East/West."
Wasu rahotanni na nuni da cewa, maharani suna magana da iyalan mutanen da aka sace, kuma har sun nemi kudin fansa Naira miliyan 40.
Ko da yake, rundunar ‘yan sandan ta ce ba ta da masaniya kan wannan batu.
“Ba mu da wannan bayani, ya kamata iyalansu su zo mu yi aiki tare domin a ceto su.” Inji Nnamdi.
Ya kara da cewa, ba za su yi amfani da karfin bindiga ba domin suna so su ceto wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar Sokoto daga yankin Niger Delta:
Your browser doesn’t support HTML5