Zanga-zangar mai taken #Revolutionnow ya gudana ne a birane da dama a kasar inda suka fito domin zagayowar shekara daya tun da suka yi zanga-zangarsu ta farko a shekarar da ta gabata.
Babban jigon zanga-zangar kuma tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya Omoyele Sowere ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, jami'an tsaro sun fito suna kokarin muzguna wa wasu masu zanga-zangar a Legas.
A wani sako na daban da shi ma ya wallafa a shafinsa na Twitter, Deji Adeyanju wanda jigo ne shirya zanga-zangar ya bayyana cewa an kama akalla masu zanga-zangar su 60 a birnin Abuja.
Hotuna da bidiyo kan shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an tsaro suka watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye, an kuma ga yadda jami'an suka wuce da wasu masu zanga-zangar a cikin mota.
Jami'an dai har yanzu ba su ce komai game da lamarin ba.
Masu zanga-zangar sun ce sun fito ne domin umartar gwamnati da ta gyara yadda take gudanar da harkokinta.