Bayan halartar jana’izar Shugaban Ma’aikatan Najeriya, Malam Abba kyari, fadar gwamnatin kasar ta dakatar da wadanda su ka halarci jana’izar daga shiga fadar na wuccin gadi.
Mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan labaru a yanar gizo, Bashir Ahmad, wanda ya na daga cikin wadanda su ka halarci jana’izar, ya tabbatar da hakan.
Yayin da hakan ke faruwa, tuni har an fara hasashe kan wanda a ke ganin Shugaba Buhari zai nada don maye gurbin Abba Kyari.
Sunan da a ka fi ambata shi ne na tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Ambasada Babagana Kingibe, sai Ministan Ilimi, Adamu Adamu da kuma na dan kasuwa Sama’ila Isa Funtua, wanda har ma ya fito ya musanta labarin.
Masani kan harkokin siyasa mai bibiyan lamarin, Dr. Abubakar Kari, ya ce hakkin nadin na wajen Shugaba Buhari kuma ya na iya soke mukamin.
Duk da muhimmancin wannan mukamin, a baya an san Shugaba Buhari da jinkiri wajen maye gurbi in irin hakan ya samu.
A saurari cikakken rahotan Saleh Shehu Ashaka:
Your browser doesn’t support HTML5