Yadda Aka Gudanar Da Zaben Gwamnoni Da Abin Da Ya Biyo Baya

Wani Malamin zabe na INEC a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya. Ranar 22 Fabrairu. 2019.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, ana can ana kidyar kuri’u bayan zaben gwamnoni na majalisun jihohi da aka yi a karshen makon da ya gabata.

Masu kada kuri’a a Najeriya, sun jefa kuri’unsu a 29 daga cikin jihohi 36 a jiya Asabar, a wannan kasa da ta fi girma a bin tafarkin mulkin dimokaridiyya a nahiyar Afirka.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an tura dumbin dakaru zuwa wasu yankuna da kuma samun hare-hare akan kayayyakin zabe.

Zaben gwamnonin, wanda aka yi shi tare da na ‘yan majalisun jihohi, na zuwa ne makonnin biyu bayan na shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka yi makonni biyu da suka gabata, wanda shugaba mai ci, Muhammadu Buhari ya samu wa’adi na biyu.

Tun da farko, an yi hasashen cewa, wannan zabe, zai kasance mai zafi a wasu sassan kasar, yayin da manyan jam’iyyun kasar ke kokarin samun rinjaye a jihohin, wadanda wasunsu, suke da kasafin kudin da ya fi na wasu kasashen Afirka.

Kudu Maso Kudanci

A Jihar Rivers da ke fama da tashe-tashen hankula, jihar da ke kudancin Najeriyar, rahotanni sun ce an jibge dakaru da dama.

“Zabe ya gudana, amma an kashe mutane biyu, har da tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC, ‘yan bindiga ne suka harbe ta.” Wani mazaunin yankin ya fadawa wakilin Muryar Amurka a yankin na Niger Delta, Lamido Abubakar Sokoto.

Rahotanni na cewa a jihar Akwa Ibom, an dan samu tashin hankali, inda jami’an tsaro suka harbe wani mutum da ya yi yunkurin sace akwatin zabe

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda jihar Rivers, Mr. Emoni Nnamdi, ya ce an baza sama da jami’an tsaro dubu 50 a yankin.

Hukumomin cikin gida, sun tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, an kona wasu kayayyakin zabe a jihar Benue da ke tsakiyar arewacin Najeriya da kuma jihar Ebonyi da ke kudanci.

Arewa Maso Gabashi

A can jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram, rahotanni sun ce an samu yunkurin da wasu mahara suka yi na kai hari a karamar hukumar Mafa.

Amma bayanai sun yi nuni da cewa an dakile harin, wanda ake tunanin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi kokarin kai shi.

“Jiya, an kawo ma su hari, amma ba tsoro ba gudu, sun fito kwansu da kwarkwatarsu sun kada kuri’arsu. Zuwanmun nan, zai karawa jama’a kwarin gwiwa.” Inji gwamnan jihar Kashim Shettima, wanda ya zai kammala wa'adinsa na biyu.

Takarar gwamna a jihar ta Borno, ana yi ne tsakanin dan takarar APC, Farfesa Babagana Ummaru Zulum da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Alhaji Muhammad Imam.

A jihar Adamawa da ke makwabtaka da jihar ta Borno, yanzu haka da alama za ta leko ta koma, game da zaben gwamnan jihar.

Daya daga cikin jam'iyyu 29 da suka tsaya takara a jihar, na zargin hukumar zabe INEC, da cire tambarin jam'iyyar a kan takardar zabe.

Sai dai da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz, ya tuntubi kwamishinan hukumar zaben ta INEC, a jihar Adamawan, Barrister Kassim Gana Gaidam, ya ce ba su da masaniya, don haka babu abin da za su ce a yanzu.

A jihar ta Adamawa, gwamna Bindo Jibrilla na neman wa’adi na biyu.

Rahotanni kuma daga Taraba na cewa a na ci gaba da hada sakamakon zaben, koda yake an koka a wasu yankunan jihar kan yadda zaben ya gudana.

Arewa Maso Yammaci

A Jihar Jigawa kuwa, dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, Malam Ibrahim Ningim ya yaba da yadda aka gudanar da zaben.

“Ya zuwa yanzu dai komai yana tafiya yadda ya kamata, duk da cewa kasan shi zabe ba ya rasa dan kuka can da dan ciwo can." Inji Ringim.

Ringim na karawa ne da gwamna mai ci, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, wanda shi ma ya yaba da zaben da aka yi.

“Kamar dai yadda muke ji, abubuwan suna tafiya da kyau, kuma mutanenmu da suke dawowa daga wajen zabe, suna gayamana cewa da yardar Allah, akwai nasara.” Inji Badaru.

A Kano kuwa, wacce ke makwabtaka da jihar ta Jigawa, a jiya Asabar, wasu mutane sun fita kan tituna suna murnar samun nasara a zaben, lamarin da ya sa hukumar zaben ta fitar da sanarwar cewa babu sakamko ko daya da ya shiga hannunta, saboda haka mutane su koma gidajensu.

Rundunar 'yan sandan jihar ma ta yi Allah wadai da hakan, inda ta gargadi masu yunkurin ta da zaune tsaye.

Zaben na jihar Kano, ya ja hankalin jama’a da dama yayin da gwamna Ganduje mai ci na jam’iyyar APC ke neman wa’adi na biyu, shi kuma Abba K. Yusuf na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke kalubalantar shi.

Jama’a da dama a jihar ta Kano na ganin takarar ta fi zafi ne tsakanin wadannan manyan jam’iyyu biyu, ko da yake, akwai Malam Sagir Takai na jam’iyyar PRP da shi ma ake ganin zai taka rawar gani.

Wani abu da ya fito karara a wannan zabe na gwamnoni a sassan da aka yi zaben, shi ne, yadda aka samu karancin fitar masu kada kuri’a, lamarin da rahotanni suka ba da dalilai da dama.

Misali, a yankin Niger Delta, bayanai sun yi nuni da cewa jami’an tsaro da aka jibge, su suka hana masu kada kuri'a fita rumfunan zabe.

Amma sabanin hakan, a jihar Sokoto, wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna, ya ce a wasu rumfunan zaben, adadin mutanen da suka fita, har ya fi na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi makonni biyu da suka gabata.

Takarar mukamin gwamna a jihar ta Sokoto wacce ita ma ta zafafa, ana yi ne tsakanin gwamna Aminu Waziri Tambuwal mai ci na jam’iyyar PDP da kuma tsohon mataimakinsa Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC mai hamayya.