Yadda Aka Gudanar Da Ranar Duniya Ta Na’urorin Fasahar Zamani

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar 4 ga watan Mayu, rana ce da aka kebe a matsayin ranar Duniya ta na’urorin fasahar zamani masu kawo saukin rayuwa. Farfesa Mukhtar Ahmad Gadanya, kwararre a fannin lafiyar al'umma da ke aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya yi karin bayani a game da fasaha mai taimakawa inganta rayuwa.