Hukumomi a Saudiyya sun dakatar da yin sallah a masallatai a wani mataki na ganin an dakile yaduwar cutar Coronavirus.
Sallolin sun hada da sallar Jumu'a da ake yi mako-mako da kuma salloli biyar da ake yi a kowace rana a masallatan.
An dauki wannan matakin ne domin hana yaduwar cutar wacce a yanzu ta kama mutum 171 a kasar.
Makwabciyarta Oman ita ma ta dauki wani mataki makamancin wannan inda ta rufe masallatai, gidajen cin abinci, shagunan siyan kayayyaki da dai sauransu.
Shagunan da aka bari bude a Oman din sun hada da na siyar da kayan abinci da kuma magunguna.
Kamfanin Dillancin Labaran SPA ya ruwaito cewa, matakin na hana sallah a duk wani masallaci a Saudiyya ba zai shafi manyan masallatan kasar guda biyu ba, wato masallatan Harami na Makkah da na Madina.
A yanzu hakan an umarci kowa a kasar da su gudanar da sallolinsu a gidajensu.
A 'yan kwanakin nan, Saudiyyar ta dauki tsauraran matakai domin ganin an dakile yaduwar cutar da suka hada da hana yin Umrah, Hajji, rufe makarantu da kuma dakatar da dukkanin jiragen saman da ke zuwa daga kasashen waje.