Sai dai hakan ya biyo bayan shimfida wasu ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar wanda cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ta fitar da kuma hukumar sufurin jirage ta kasar.
Daya daga cikin jiragen da suka sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa wato Nmandi Azikwe Int'l Airport dake babban birnin tarayyar kasar Abuja, daga Legas ya taso.
Yanzu jihohi biyu ne gwamnatin kasar ta ba da umarnin filayen jiragensu su soma aiki daga ranar 8 ga watan Yuli, tun bayan sama da watanni uku da aka dakatar da duk wata zirga zirga da ta shafi jiragen.
A cewar Kyaftin Rabiu Yadudu da ke zama babban shugaban hukumar filin jirgin sama ta Najeriya, "an dauki matakai da dama kuma an bai wa ma’aikata da ke wajen horo na musamman kana a shirye suke don tabbatar da an kare lafiyar al’umma."
A ranar 11 ga wannan wata na Yuli ake sa ran filin jirgin sama na Malam Aminu kano dake jihar Kano da na Port Harcourt da Owerri hada da Maiduguri za su soma aiki yayin da a ranar 15 ga watan sauran filayen jiragen sama a sauran jihohin kasar suma za su soma aiki.
Idan za a tuna tun a watan Maris gwamantin Najeriya ta ayyana dakatar da dukkan hada-hadar sufurin jiragen sama sakamakon bullar cutar coronavirus a kasar, wanda ya zuwa yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura dubu 29,789 ya kuma yi sanadin mutuwar mutane 667 kana mutane 12,108 sun warke daga cutar.