Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa ‘ya zuwa an tabbatar da samun mutum uku na farko da ke dauke da sabon nau'in cutar Korona na Omicron a cikin kasar.
Cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar tun da farko da ke dauke da sa hannun Dr Ifedayo Adetifa, da ke zama Direkta Janar na hukumar, an bayyana cewa hukumar ta NCDC an gano nau'in cutar a jikin fasinjoji biyu da suka shigo Najeriya daga kasar Afirka ta kudu ta hanyar amfani da fasahar gano tsarin kwayar halita ta 'genomic sequencing' a Abuja, babbar birnin tarayyar Najeriya.
Da safiyar yau Laraba ne hukumar ta sanar da cewa adadin ya karu da mutum daya, a cewar hukumar dai wannan yunkuri na binciken da ake ta yi ya biyo bayan ayyana nau'in cutar na Omicron a cikin jerin cututtuka da ake yi wa kallon 'abin damuwa da kuma firgita kasashen duniya da hukumar lafiya ta duniya ta yi
Hukumar ta NCDC dai ta tabbatar da cewa tuni aka fara gudanar da muhimman bincke game da wadanda suka yi mu’amala da mutanen da ke dauke da wannan cuta don saurin dakile ta a kasar la’akari da yanda nau’in cutar ke saurin yaduwa a wasu kasashe da aka samu bullarta a cikinsu.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana sabon nau'in cutar Korona na Omicron a matsayin "hadari mai girma" a duniya kuma akwai yiwuwar yaduwarsa duk da cewa ba a san yadda sabon nau'in ke yaduwa ba, yanayin hadarinsa ko yiwuwar jin rigakafi.
A halin yanzu, nau'in Korona na Omicron ya riga ya fara yaduwa a kasar Netherlands lokacin da Afirka ta Kudu ta sanar da WHO game da hakan a makon da ya gabata,
A ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 2021, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasar Afrika ta kudu (NICD) ta bada sanarwar gano sabon samfurin COVID-19 wato B.1.1.529 wanda daga baya aka yi wa lakabi da Omicron, Wanda ake ganin shi a matsayin ‘dan auta a gidan cutar murar mashako ta Coronavirus da ta bayyana a shekarar 2019.
Tuni dai Hukumar lafiya ta Duniya ta sa wa wannan samfuri suna Omicron, kuma ta tabbatar da hadarin cutar saboda irin yadda ta ke yawan hayayyafa da yaduwa cikin kankanin lokaci.