Ya Yiwa 'Yarsa Mai shekaru 16 Fyade

Wata kotun majistire dake zama a Ikeja a jihar Legas na tuhumar wani mutun mai shekaru hamsin da biyu mai suna Paul Akpederi da laifin yiwa yarshi mai shekaru goma sha shida fyade.

An tuhumi Akpederi da laifin yin amfani da yarinyar ta haramtacciyar hanya.

Inda sufeton yan sanda Simon Imhonwa ya sanar wa da kotu cewa wanda ake tuhuma ya soma aikata laifin ne tun shekarar dubu biyu da sha biyu a unguwar Ikorodu dake jihar Legas.

Ya kara da cewa hukuncin laifin ya sabawa sashi na 137, na kundin lafuffukan jihar Legas. Wanda ake kara kuma ya amsa laifinshi a gaban kotu.

Lauya mai kare wanda ake karar A. O Gbadomosi ya roki kotu da ta bayar da dama domin a duba lafiyar kwakwalwar wanda ake tuhuma. Inda ya kara da cewa wanda ake zargin na Magana da kanshi tare da ihu shi kadai.

Saidai lauya mau saurarar karar bai amince da wannan rokon ba inda yace ya kamata ace anyi wannan tun maganar tana hanun yan sanda. Mai shari’a Osinsanmi ya bada belin shi akan zunzurutun kudi Naira dubu dari biyar da kuma masu tsaya mishi guda biyu wanda kuma suka kasance yanuwansa ne.

Osunsanmi ya kara da cewa tilas sai an nuna shaidar biyan haraji a jihar legas daga bisani ya daga karar zuwa 6 ga watan Disamba.