Ya Yiwa 'Yar Shekaru 4 Fyade

Wani matashi mai suna Najite Odibie mai shekaru talatin da haihuwa wanda ake zargi da yiwa wata ‘yarinya mai shekaru hudu fyade, yayi batar dabo.

Wannan abin ya faru ne a Otovwodo, a karamar hukumar Ughelli, ta arewa dake jihar Delta,inda matashin ya yaudari yarinya da biskit zuwa turakarsa inda ya aikata mata aika aika.

Mahaifiyar yarinya tace ta ga wani farin abu a gaban ‘yarta da ta tambaye ta sai yarinyar tace Najite, ne ya aikata mata.

Ta kara da cewa da suka tukari Najite, da batun bai karyataba daga bisani sai aka kai yarinya asibiti kuma aka kai maganar gaban ‘yan Sanda, kafin ‘yan Sanda su isa gidan Najite Odibie, ya bita rufin dakinsa ya ranta ana kare.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Delta, DSP Andrew Aniamaka, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce rundunar na yin duk abinda ya kamata domin ganin cewa an damke Najite Odibie, an gurfanar dashi a gaban kuliya.