Diya Ko Kuma Jika Za A KIra Ta?

Wata mata 'yar jihar Texas a Amurka, mai shekaru 54 da haihuwa ta haifi jikarta bayan da ta dauki juna biyun diyarta.

Sunan jaririyar da aka haifa Kelcey, wacce za a ce kakarta Tracey Thompson da mamarta Kelley McKassack suka haifa.

Biyo bayan barin da Kelley ta yi har sau 3, ya sa mahaifiyarta Mrs. Thompson yanke shawarar daukarwa diyar ta ta ciki. Ma'ana, likita zai hada kwan diyar da na mijinta sai ya sa a mahaifar uwar, ko kuma duk lokacin da diyar ta dauki ciki, likita zai iya cirewa ya sawa uwar, abinda ake kira "surrogate" a turance.

Mrs Thompson ta fadi cewa, "shekaru 15 da suka wuce, diyarta Kelley ta taba tambayarta cewa, in ta kasa haihuwa da kanta ko uwar za ta yarda ta daukar mata cikin? uwar ta ce babu damuwa, sai ga shi abin ya faru da gaske.

Mrs Thompson na da wani da mai shekaru 30 da haihuwa bayan Kelley, kuma ta na da jika dan shekaru 3.

Unguwar Mrs, Thompson da diyarta babu nisa sosai, su duka biyun sun kula da juna biyun tamkar ma Kelley ce ke dauke da cikin, duk lokacin da Mrs. Thompson za ta awo asibiti da Kelley a ke zuwa. ko lokacin da uwarta haihu, Kelley, ta nan tare da ita a dakin haihuwa.

Mrs. Thompson ta kuma ce mawuyacin abu ne daukar ciki a shekarunta saboda jikinta ya kwan biyu. bayan haka ta yabawa mijinta don goyon bayan da ya bata har lokacin da ta haihu.

Iyalin Mrs. thompson sun ce idan jaririya Kelcey ta girma za su gaya mata yadda aka dauki cikinta da kuma yadda aka haife ta. Bayan haka sun yanke shawarar cewa Kelcey za ta kira Mrs. Thompson da ta haifeta Kaka, Kelley kuma Mama.