Ya Kyautu Al'umar Ile Ife Suyi Karatun Ta Natsu

Kungiyar masu sana’ar sayarda kayan miya daga arewacin Najeriya zuwa kudanci wadanda aka fi sani da masu sana’ar kayan Gwari ta Najeriya, rashen jihar Oyo, tace zata taimakawa wadanda rikicin Ile Ife, ya shafa.

Shugaban kungiyar Usman Yako, wanda ya shaida hakan ya kuma bukaci masu hannu da shuni dasu taimaka wajen tabbatar da cewa wadannan mutane da balai ya afkawa sun samu sa’ida ta duk fuskokin taimako da za a iya domin agaza masu.

Shima mataimakin shugaban Akanbi Olawiyola, ya bukaci mutane Ile Ife, da suyi karatun ta natsu su zauna da juna lafiya, yana mai cewa kabilanci ba nasu bane, yace zaman Hausawa, Yarbawa, Fulani, Barebari da sauran kabilu tare ya zama wajibi.

Olayiwola, ya kara da kiran al’umar Ile Ife, dasu rungumi juna hannu biyu biyu su kuma tabbatar da cewa Ba’raka bata shiga tsakaninsu ba domin zaman tare shine samun ci gaban kowace al’uma.

Your browser doesn’t support HTML5

Ya kautu Al'umar Ile Ife Suyi Karatun Ta Natsu - 3'13"