Ya Kashe Shi Da Kwalba Saboda Indomie

Kwalba

Wata kotu a Akure, ta bada umarnin da a tsare wa mai askin barber, Oluwaseun Ojo, dan shekaru 25, a gidan yari saboda zargin sa da ake yi da kisan abokinsa Shola Omotayo.

Mai sharia Mr. Sunday Adedapo, ya ce mai laifin ya ci gaba da zama a gida kurkukun Olokuta, har zai kotu ta ji daga ofishin mai gabatar da kara.

Da yake bada shaida mai gabatar da kara ASP Pelumi Adejuwon, ya ce Oluwaseun Ojo, da abokinsa Shola Omotayo, sun fara gardama ne akan Taliyar Indomie, daga bisani ta kai Ojo, ya fasa kwalba ya dabawa abokinsa a kirji da baya, abunda yayi sanadiyar mutuwar sa.

Mai gabatar da karar Adejuwon, ya kara da cewa laifin ya sabawa sashe na 316, na dokar laifuffuka na jahar Ondo.