Ya Kamata INEC Ta Soke Zaben 'Yan Majalisun Jihar Pilato

An yi kira da hukumar zabe ta kasa da ta soke zaben da aka gudanar a jihar Pilato, na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a makon jiya.

Wasu daga cikin 'yan jam’iyyar PDP a shiyyar tsakiyar jihar Pilato sun yi kira ga hukumar zabe da ta soke zaben ‘yan majalisun tarayya a yankin. Kamar yadda jami’in tattara kuri’u a yankin ya gabatar, saboda wasu matsaloli da suka gano a rumfunan zabe guda tara a karamar hukumar Kanam.

Hukumar zaben dai ta ayyana cewa jam'iyyar APC ce ta lashe zaben kujerar sanata da na dan majalisa a yankin ba tare da bayyana yadda aka warware matsalolin ba.

A halin da ake ciki dai hukumar zaben zata gudanar da zaben sanata a daukacin shiyyar kudancin jihar ta Pilato, da na dan majalisan Jos ta Arewa da Bassa a majalisar tarayya duk daga bangaren jihar Pilato ta Arewa.

Ga rahoton wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Ya Kamata INEC Ta Soke Zaben 'Yan Majalisun Jihar Pilato 3'10"