Alhaji Abubakar Dangulguli, shugaban kungiyar Matasan Nigeria da ake cewa NYO a takaice yace, ranar matasa rana ce mai muhimmanci ga matasan duniya ga baki daya, saboda rana ce wadda za'a tabbatar wa duniya cewa an bar matasa a baya a harkokin siyasa dana tattalin arziki. Harkokin daya kamata matasa ne jagorancin su.
Akan furucin da baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon yayi cewa ba'a taba bukatar gudumawar matasa a duniya kamar a wannan lokaci mai sarkakiya ba.
Alhaji Abubakar yace Mr Banki Moon yayi wannan furuci ne a saboda yanayin da duniya ta samu kanta a ciki na rashin zaman lafiya da lalacewar tattalin arziki.. Alhaji Abubakar Dangulguli yayi wannan furucin ne a hirar da Ibrahim Ka Almashi Garba yayi dashi
Matasa sune wadanda aka barsu a baya, wadanda kuma ake amfani dasu wajen kawo tashe tashen hankula. Domin ana rabewa da guzuma, ana anfani da rashin aiyukan su da kuma talauci da ya yi musu kanta.
Alhaji Abubakar yace yanzu ne ya kamata gwamnitocin kasashen duniya su yi amfani da matasa, su basu abun yi, su basu illimi, kuma su tabbata cewa sun taimaka musu, domin kada su sa kasashen duniya cikin tashin hankali.
Your browser doesn’t support HTML5