Ya Guntulewa Matarsa Kunne Da Cizo

Wata kotu a Kano, ta bada umarni a tsare wani matashi, mai shekaru talatin da ukku, mai suna Abubakar Ali, a gidam yari har zuwa ranar ashirin da shida ga wannan watan.

Shi dai Abubakar Ali, wanda yake zaune a Tundun Yola, a birnin Kano, an tuhumarsa ne da laifin zalunci da azabtarwa ta hanyar cizon matarsa a kunne har sai da kunnen ya guntule.

Mai gabatar da kara Sufeton ‘yan Sanda Yusuf Sale, ya fadawa kotu cewa a ranar biyar ga wannan watan na janairu wata mata mai suna Hadiza Ibrahim, wace suke zaune a gida daya ne ta kawo kara Ofishin, ‘yan Sanda dake rijiyar Zaki, cewa wani mai suna Abubakar Ali ya guntulewa matarsa kunne ta hanyar cizo.

Ma’auratan dai sun samu wata ‘yar takaddama ce sai daga bisani abin ya kazance ta kai ga har aka guntule kunne, koda yake Abubakar Ali, ya amsa laifinsa amma Alkali Aminu Fagge, y adage shara’ar har zuwa ashirin da shida ga wannan watan.