Ya Bukaci Da Ayi Amfani Da Basirar Matasa

Dr. Khalifa Dikwa (Sarkin Malamai)

Kafa hukumar raya arewa maso gabashin Najeriya, wanda rikicin Boko Haram, ya daidaita abune da ya kyautu ace an yin tutuni ganin irin halin da jama’ar yankin suka sami kansu a ciki.

Wani Malamin jami’a Dr. Khalifa Dikwa, ne yayi wannan tsokacin a wata hira da yayi da muryar Amurka.

Malamin ya ce yakamata a tabbatar da cewa jihohi da abin ya shafa an kula dasu kamar yadda yakamata

Dr. Khalifa, ya umarci jama’a su dauki kadara akan halin da suka shiga biyo bayan hare haren kungiya ta Boko Haram, a yankin baki daya.

Ya kuma shawarci mahukuntan wannan hukumar dasu hanzarta gudanar da aikace aikacen su a wannan yankin kuma a guji sa siyasa a harkokin hukumar.

Ya bukaci da’a yin amfani da basirar da Allah ya yiwa dimbin matasa da Allah ya azurtamu dasu wajan gudanar da aiyukan da suka kamata.