Xi Jinping Ya Yi Kashedi Akan Illar Jayayya A Fannin Cinakayya

Switzerland Davos Forum

Shugaban China Xi Jinping ya yi kashedi ga gwamnatoci game da illar jayayya a fannin cinakayya, a yayin da ya ke jawabi a wani taro kan tattalin arzikin duniya a Davos, kasar Switzerland a jiya Talata.

"Kare cinakayyar gida tamkar rufe kai ne a daki mai duhu. Ta haka ana iya kare kai daga iska da ruwa, to amma ta hakan kuma ana iya rasa haske da iskar shaka," a cewarsa a jawabin, wanda ga dukkan alamu da Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ke yi, ganin ya sha alwashin saka harajin kashi 45% kan kayakin China da ke shigowa Amurka, da kuma kashi 35% kan motocin Jamus da aka kera a kasashen ketare.

Xi ya kuma yi nuni da dinbin albarkatun da kasar China ke da su, don jaddada cewa kasar na iya samar da hada-hadar kasuwanci sosai ga kasashen da ba su adawa da ita.

Kasar China za ta kashe dala tiriliyan 8 wajen shigo da kayakin waje sannan kuma ta kashe dala biliyan 750 a harkokin kasuwanci a kasashen ketare; Chinawa 'yan yawon bude ido za su yi tafiye-tafiye har wajen miliyan 700 da za su taimaka ma tattalin arzikin duniya, cikin shekaru biyar masu zuwa, a cewarsa.