Xabi Alonso, Ya Shiga Sahun Limaman Tamola A Duniya

Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Real Madrid, Xabi Alonso ya zamo mai horas da kulob din Real Sociedad, bangaren matasa (Team B).

Alonso wanda ya lashe gasar zakarun turai Uefa Champios league tare da kungiyar Liverpool da kuma Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 37 da haihuwa ya buga wasa a kungiyar ta Real Sociedad sau 124, ya kuma taimaka wa kulob din zuwa gasar cin kofin zakarun turai a 2003 zuwa 2004, kafin daga bisani ya koma Ingila da fafata wasa a Liverpool daga 2004/05.

Tsohon dan wasan tsakiyar na kasar Spain ya dawo kasar sa ta haihuwa inda ya hade da kungiyar Real Madrid a 2009, daga karshe ya koma Bayern Munich na kasar Jamus inda anan ya ajeyi takalman taka ledarsa a shekara ta 2007.

Ya karbi aikin maihoras da Matasan Real Sociedad ne bisa yarjejiniyar kwantirakin shekaru biyu.