WHO: Ta Yaba Da Matakan Da China Ta Dauka Na Shawo Kan Cutar Coronavirus

A yayin da kasar China ta bayyana cewa ana ci gaba da samun raguwar adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus, jami'an hukumar kiwon lafiya ta duniya sun yaba da irin matakan da kasar ta dauka wajen shawo kan cutar tare da yin kira ga sauran wasu gwamnatocin kasashe akan su daura damarar yaki da cutar idan ta bulla a kasashensu.

Jami'an kiwon lafiya a China sun ce, a yau Laraba an sami mutane 406 da suka kamu da cutar, kusan dukkan su a lardin Hubei suke inda annobar ta fi kamari. Duka mutane 52 da suka mutu kuma a kwanan nan a lardin na Hubei suke, yankin da aka killace tsawon makwanni don dakile yaduwar kwayar cutar zuwa sauran yankuna.

Bruce Aylward, wanda ya jagoranci wani shirin hadin gwiwa tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya da China game da cutar, a lokacin wani taron manema labarai ya ce, yayin da aka sami bullar cutar a kasashe sama da 30, yanzu har da kasashen Turai da Gabas ta Tsakiya a wannan makon, dole ne gwamnatoci su dinga nazarin saurin gano wadanda suka kamu da cutar, da nemo mutanen da suka yi mu'amalla da wadanda ke dauke da cutar, da kuma daukar matakan kebewa don hana yaduwar kwayar cutar.

A halin da ake ciki kuma, bayanin da gwamnatin Amurka tayi game da tashin hankalin cutar coronavirus dake kara zafafa ya kawo rabuwar kawuna a tsakanin 'yan majalisar kasar a jiya Talata, yayin da 'yan jam'iyyar Democrat dake majalisar suka nuna rashin amincewarsu da bayanin da Shugaba Donald Trump yayi cewa an dauki matakan magance cutar a Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump

A jiya Talata ne Trump ya ce, Amurka ta dauki matakan kariya da magance cutar sosai” a kasar, duk da cewa gwamnatinsa na neman majalisar dokokin kasar ta amince a bata kudi dala biliyan biyu da dago biyar don daukar matakan gaggawa na magance matsalar.

Dr. Nancy Messonnier

Nancy Messonnier, darektar Cibiyar kula da harkokin rigakafi da cututtukan numfashi a hukumar kiyaye yaduwar Cututtuka ta Amurka, ta ce, ya zuwa yanzu an sami nasara a kokarin kiyaye bazuwar cutar." Amma ta yi gargadin cewa yayin da ake samun rahotannin bullar cutar a kasashe da yawa kuma wasu ba su san yadda suka kamu da cutar ba, dakile shigowar cutar Amurka zai zama da wahala.