Wayne Rooney Yayi Watsi Da Tayi

Wayne Rooney

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal mai suna Hector Bellerin, ya sake rattaba hannu a kungiyar na tsawon shekaru shida masu zuwa wannan dan wasa dai Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Manchester City na zawarcinsa.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham dake kasar Ingila na shirye shirye domin kara wa mai tsaron ragarsu Hugo Lloris kwantaregi na tsawon shekaru biyu nan gaba.

Alexis Sanchez, na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, yaki amincewa da tayin da wata kulob ta masa a kasar China.

Shima dan wasan gaba na Kungiyar Manchester United, kuma kaftin a kungiyar Wayne Rooney yayi watsi da tayin da wata kungiya mai suna Beijing Guon dake kasar China tayi masa kungiyar dai tana bukatar Rooney da ya koma a tsakiyan kakar wasan bana da zaran anbude hada hadar saye da sayarwar ‘yan wasa a watan janairu na shekara 2017.

Your browser doesn’t support HTML5

Wayne Rooney yayi watsi da tayin da wata - 1'09"