Hukumar ‘yan sandan kasar Ingila ta na tuhumar tsohon jagoran ‘yan wasa kwallon kafa na kasar Ingila mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Everton, Wayne Rooney, bisa tuki cikin maye.
Hukumar ‘yan sandan bangare Cheshire sunce an kama dan wasan ne a kan hanyar Altrincham, bayan da wani jami’in ‘yan sandan ya tsayar dashi sai ya gano cewar Rooney, ya kwankwadi barasa fiye da kima.
Yin haka kuma ya saba wa dokar kasar Ingila.
Bayan yan sandan sun tafi dashi ofishinsu daga bisani Wayne Rooney, ya Koma gida bayan an karbi belinsa.
Sai dai zai gurfana a gaban kutun, nan ba da jimawaba a cikin wannan watan na Satumba da muke ciki na shekara dubu biyu da sha bakwai.
A satin da ta wucene dai Rooney, ya bada sanarwar ajiye takalmam taka ledarsa wa kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila bayan ya shafe shekaru sha hudu yana murza wa kasar leda a mataki daban daban.
Your browser doesn’t support HTML5