Waye Ya Lashe Gasar Kamun Kifi Ta Argungu?

Abubakar Ya'u, (tsakiya) mutumin da ya lashe gasar kamun kifi ta Argungu (Hoto: Gwamnatin jihar Kebbi - Facebook)

Abubakar Ya’u dan asalin jihar Kebbi ya lashe gasar kamun kifi ta kasa da kasa ta Argungu bayan da ya kama kifi mai nauyin kilo 78.

A jiya Asabar aka ayyana Ya’u a matsayin wanda ya lashe gasar wacce aka kwashe kwana hudu ana wasannin a garin Argungun da ke jihar ta Kebbi inda daga bisani aka kammala ta da wasan kamun kifin.

Akalla masunta 30,000 ne suka nuna bajintarsu ta kamun kifi a gasar wadanda suka fito daga Najeriya da mawabciyarta Jamhuriyar Nijar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Bala Yahaya wanda shi ma dan jihar Kebbin ne, shi ya zo na biyu da kifi mai nauyin kilo 75 kana Maiwake Sani daga Sokoto ya zo na uku.

An ba Ya’u kyautar N10 miliyan da motoci biyu da kuma kujerar maka biyu, a cewar jaridar Daily Nigerian.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya na NAN ya ce masunta sama da 50,000 ne suka kara a gasar wacce aka saba yi a kowace shekara.

Ko da yake, an dakatar da gasar har na tsawon sama da shekara 10 saboda dalilai na tsaro – amma aka dawo da ita a bana.

Yayin rufe gasar, Sarkin Argungu, Isma’ila Muhammad Mera ya ce dawo da gasar, alama ce da ke nuna cewa zaman lafiya ya samu.