A ranar Juma’a ake sa ran kamfanin Samsung zai fitar da sabuwar wayar Galaxy Z-Flip, wayar mai tsarin malam bude mun littafi, da ke budewa da kullewa. Wannan shine yunkurin kamfanin na biyu don sayar da wayoyin hannu masu kawa.
Kamfanin ya sanar da hakan ne a farkon wani taron da ya gudana a birnin San Francisco. Sabuwar wayar zata iya budewa daga karamin murabba'in sama zuwa matsayin wayar salula ta gargajiya, kuma za a fara sayar da ita a kasuwa daga ranar 14 ga watan Fabrairu a kan kudi dalar Amurka $1,380.
An dai fara sayar da wayar ta Samsung mai karba-karba ta Galaxy, tun a watan Satumbar da ta gabata, bayan jinkiri da aka samu na matsalar da wayar ke dauke da ita na fashewar allo.
Waada aka sayar da ita akan kudi dala Amurka $2,000 a lokacin, amma yanzu kudin ta ya ragu. Kamfanin Motorola ma ba a barsu a baya ba wajen kera irin wannan wayar da suka yi mata farashi na dalar Amurka $1,500.