Abin al’ajabi bashi karewa, sabuwar fasahar wayar hannu ta zamani ta nuna yadda wata waya da kamfanin kasar China yak era, wadda za a iya nunkewa da kuma warwareta ta yi fadi domin amfani da ita a matsayin ipad.
Wannan waya nada kyamarar daukar hoto mai idanu (lense) guda tara, kuma tana daukar hoto mai nau’uka daban daban, kama daga mai nau’in fari da baki, mai kala da sauran su.
Girman wannan waya bai banbanta da na sauran wayoyi ba, amma mutum zai iya bude ta kamar shafin littafi ta zama da fadi domin amfani da shafukan yanar gizo, haka-zalika da mai ita ya dora yatsan sa akan gilashin, zata bude kanta da kanta.
Abin ba a cewa komai, domin kuwa sababbin dabaru da mahajojin da wannan waya ke dauke da su, sun wuce misali sai mutum ya gani da idon sa.